Umaru Bago Tafida

Umaru Bago Tafida
Rayuwa
Haihuwa 1954 (69/70 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a

Umaru Bago Tafida III (an haife shi a shekarar ta alif Dari Tara da hamsin da hudu 1954) shi ne sarki na 12th, na Etsu, ko kuma sarkin gargajiya na Masarautar Lapai a jihar Neja, Najeriya. An naɗa shi a watan Yuli shekarar 2002. Ya gaji Sarki Alhaji Muhammadu Kobo, wanda ya rasu yana da shekaru 92 a duniya bayan ya yi mulki na tsawon shekaru 48, kuma gwamnan jihar Neja Abdulkadir Kure ya nada shi kan kujerar sarauta.

A lokacin bikin nadin Umaru manyan mutane da dama sun halarci taron naɗa mashi rawanin ciki harda mataimakin shugaban ƙasa na wancan zamanin wato Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Ibrahim Babangida.


From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy